KUNDIN TSARIN MULKI DA MANUFOFIN CIBIYA

BAIRUHA FEMALE RELIEF FOUNDATION (cibiyar tallafawa mata mabukata da masu rangwamen gata)

 

TAKENMU: Duk wanda ya taimaki wani. . . . .

 

 

ADIRESHI: Gini Mai Lamba 22, Unguwar Tudun Maliki, Farkon layin Torrey Home, Titin Gidan Zoo, Jihar Kano, Najeriya.

 

 

E-MAIL: bairuhafemalerelief@gmail.com

 

FACEBOOK PAGE: Bairuha Female Relief Foundation

 

TWITTER: @bairuhafrf

 

INSTAGRAM: bairuhafrf

 

WHATSAPP: 0802 244 6446

 

 

BAIRUHAFRF

wannan Cibiya mai suna a sama da ke unguwar tudun maliki, karamar hukumar Kumbotso, zamu tallafa tare da taimakawa mata mabukata a duk inda suke a fadin jiharmu ta Kano a bisa wadannan kaidoji, kamar haka:

 1. Za mu gudanar da ayyukanmu tsakani da Allah gwargwadon bukata ko matsalar mace.
 2. Haka kuma mun tsarawa kanmu wani tsarin mulki don tafi da wannan cibiya tamu, da kuma cimma burinmu wajen ci gaban yan uwanmu mata da basu kariya da taimako don yaye wani daga cikin kuncin da suke ciki, da walwalar su data ‘ya’yansu, da karfafa zukatansu.
 3. Yin bincike don gano mabukata na hakika da basu tallafi gwargwadon abinda zai cicciba rayuwarsu, don hana iyaye tura ‘yammata tallace-tallace saboda talauci.
 4. Akwai samawa mata guraben karo ilimi don sanin rayuwarsu da abubuwan da zasu dogara dashi don kula da tarbiyyar yayansu.

 

MANUFOFIN WANNAN CIBIYA

 1. Rage wa mata kangin talauci da wahala ko tabewa.
 2. Koyar da mata sana’o’in hannu don dogaro da kai.
 3. Samawa mata guraben karo ilimin addini dana zamani.
 4. Kyautata rayuwar matan da take cikin garari da tozarta.
 5. Samar da tallafi ga matan da jarinsu ya durkushe ko yake kan gargar, ko kuma samar da tallafin jarin a karon farko.
 6. Bunkasa sana’o’i da hanyoyin samun abin rufin asiri ga matan da basu da madogara.
 7. Ruguza dabi’ar tallace-tallace da yawace-yawace da barace-barace ga yan uwanmu mata ta kowanne hali.

 

 

MAJALISAR ZARTARWA DA TSARINTA

Wannan Cibiya, bayan manufofi tana da tsarin zartar da aikace-aikacenta, don samun damar gudanar da ita yadda ya kamata ba tare da zabe ko son kai ko nuna fifiko da sanayya ba.

 

 

AYYUKAN MAJALISAR ZARTARWA

Alhakin aiwatarwa da manufofin Cibiya ya rataya a wuyan jagororin wannan Cibiya.

Majalisar zartarwa ke da alhakin nada kwamitoci da membobi.

 

 

SHUGABANNI DA AYYUKANSU

 

SHUGABA:

 1. Itace babbar jagora ta wannan Cibiya, babbar mai fada a ji a tsarin mulki da gudanarw, bugu da kari, dukkan tsare-tsare da kudurce-kudurce da aikace-aikace daga ofishinta zai dinga fitowa.
 2. Ita zata shugabanci majalisar zartarwa.
 3. Ita zata sa hannu akan kowacce takardar ziyarar binciken bada tallafi, ko duba hali da yanayin wadanda suke bukatar tallafi.
 4. Sai da amincewarta za’a gudanar da komai na cibiya.
 5. Itace ke da alhakin tsarawa da jagorantar kai ziyarar bazata ga unguwanni.
 6. Hakkinta ne ta umarci kiran kwamitocin Cibiya na ka’ida ko na gaggawa.
 7. Gabatar da kasafin kudi ko wani abu na gaggawa.

 

MATAIMAKIYAR SHUGABA:

 1. Ita ke da damar jan Cibiya idan shugaba ba ta nan ko ofishin ba kowa.
 2. Taimakawa shugaba a dukkan harkokin cibiya.
 3. Dora mata wani aiki na musamman da majalisar zartarwa zata yi, ko kuma ita shugabar ta dora mata.
 4. Itace farkon mai sa hannu a chek (check) idan za’a fitar da kudi daga asusun cibiya ko idan za a karbi kudi.

 

BABBAR SAKATARE

 1. Ita ke rubuta ajandu, da tarurrukan Cibiya tare da amincewar shugaba.
 2. Daukar bayanai a tarurruka tare da bayanin taro na baya.
 3. Tsarawa da kuma ajiye muhimman takardun Cibiya.
 4. Rubuta takardun Cibiya na shige-da-fice.
 5. Ita ke da alhakin gabatar da duk wani kashe-kashen kudin Cibiya ga majalisar zartarwa.
 6. Ita ke tsara duk wani muhimman ayyukan Cibiya, da nasarorinta a cikin shekara domin gabatarwa.
 7. Tana daga cikin ma su alhakin sa hannu idan za a karbi kudi ko fitar dasu daga asusun cibiya.

 

MA’AJI

 1. Shi ne ke da alhakin gudanar da duk wata harka da ta shafi kudi da ajiyarsu.
 2. Shi ne ke da alhakin tara dukkan bayanan da suka shafi dukiyar Cibiya.
 3. Yana daga cikin ma su alhakin sa hannu idan za a karbi kudi ko fitar dasu daga asusun cibiya.

 

JAMI’AR BINCIKEN KUDI

 1. Ita ce ke da alhakin karbar dukkan littafin kudin Cibiya don gudanar da bincike.
 2. Ita ce zata mika sakamakon kudaden da suka shiga ko suka fita duk bayan sati biyu.
 3. Hakkinta ne binciko dukkan al’amuran kudin Cibiya, da kadarorinta a duk karshen shekara.

 

SAKATAREN YADA LABARAI

 1. Shi ne da alhakin sanar da lokutan gudanar da ayyuka ko kwamitoci.
 2. Shi ke da alhakin duk harkar da ta shafi yada labarai.
 3. Tabbatar da sanar da harkokin Cibiya ta kafar yada labarai.
 4. Shi zai shugabanci kwamitin yada labarai.

 

MAJALISAR MA SU BADA SHAWARA

Wannan Cibiya tana da majalisar ma su bada shawara wadda ta kunshi mutum uku.

 1. Su za su ba wa Cibiya shawara a duk harkokinta na ci gaba.
 2. Zakulowa da bada sunayen yankunan da suke bukatar tallafi don kafa kwamitin bincike da gano mabukata da masu rangwamen gata don tallafa musu.
 3. Ba da taimako a Cibiya ta hanyar da suke ganin za su iya.

 

 

ASUSUN CIBIYA

Wannan cibiya tana samu kudin shigarta ne ta hanyar sana’o’in da ayyukan da jagororin cibiyar suke yi, da sauran hanyoyin da shari’a ta yarda da su kamar:

 1. Taimakon daidaikun mutane ko tarin Jama’a.
 2. Taimakon karamar hukuma ko Gwamnatin jiha ko ta tarayya.
 3. Taimakon kungiyoyi masu zaman kansu wadanda hukuma ta san da zamansu.
 4. Tallafi daga masu kudi ko wadanda suke rike da madafun iko ko malamai masu shawarar taimakawa mata mabukata ko masu rangwamen gata.
 5. Hakkin yarda a karbi kudin Cibiya ya rataya ne a wuyan wadannan shugabanni: Mataimakiyar Shugaba, Sakatariya, Ma’aji.

 

A takaice wadannan sune kadan daga cikin ayyuka da tsare-tsare da gudanarwar wannan cibiya mai albarka ta mata mabukata da masu rangwamen gata, mai suna;

BAIRUHA FEMALE RELIEF FOUNDATION

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *